An Yi Amfani Da Sa Hannun Buhari Na Bogi Wajen Cire Dala Miliyan Dubu $6,230,000 Daga CBN, Cewar Tsohon Sakataren Gwamnati Boss Mustapha
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha wanda ke ba da shaida a ranar Talata, 13 ga watan Fabrairu a shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, ya ce shi ma an saci sa hannunsa, dan haka bai san komai ba game da kuɗaɗen da aka ce an fitar da su domin biyan masu sa ido kan zaɓe 'yan ƙasar waje.
"An yi amfani da sa hannun bogi na tsohon shugaban ƙasa Buhari, wajen cire Dala miliyan dubu 6,230 ($6,230,000), daga babban Bankin Najeriya CBN a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2023, in ji shi.