Ɓarnar da hukumomin jamhuriya ta bakwai suka yi babba ce. __ Jaridar Le canar en furie akan ayukkan COLDEF.

Mr blogger
0

 Ɓarnar da hukumomin jamhuriya ta bakwai suka yi babba ce.

__ Jaridar Le canar en furie akan ayukkan COLDEF. 



Mujallar ta ce wasu majiyoyin sun tabbatar ma ta cewa ,hukumar yaƙi da yiwa tattalin arziƙin Nijar zagon ƙasa ta COLDEF, ta ci karo da tulen ayykkan da sai an ɗauki tsawon lokaci kafin a samu sakamako.


Domin majiyar ta ce ,a jamhuriya ta bakwai an karkatar da sama da milyar dubu biyar a fannin ayukka.

A ma'aikatar man fetur kuma,hukumomin jamhuriya ta bakwai sun ce ,a ko wane yini ganga dubu 20 na ɗanyan mai ake fitarwa,alhalin ko ganga dubu 35 ne suke fitarwa. wanda haka ke nuna ko wane yini ganga 15 ake fitarwa ba bisa ƙa'ida ba. 



Majiyar ta ce, akwai badaƙaloli da dama da COLDEF ta gano an aikata a jamhuriya ta bakwai,wanda sai an kwashe lokaci mai tsawo kafin samun sakamako.

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)