DAN A TAIMAKI NIJERIYA AKA ƘIRƘIRI ECOWAS~ INJI TCHIANI

Mr blogger
0

  DAN A TAIMAKI NIJERIYA AKA ƘIRƘIRI ECOWAS~ INJI TCHIANI



A cikin jawabin da ya gabatar a yau, Shugaban ƙasa a Nijar Birigediya Janaral Abdoulrahmane Tchiani ya bayyana yanda ƙasashen na yammacin Afrika suka cimma matsayar haɗa kungiyar ta Ecowas a shekarar 1975, domin tallafawa Nijeriya a yanayin barazana da ta samu kanta bayan yaƙin Basansan wato Biyafara (Biafra).



Ya cigaba da cewa “Manufar ƙirƙirar kungiyar ya haɗa da samar da cikakken ƴanci da tallafi tare da tsaron rayuwa da dukiyar Al'ummar kasashen. Sai dai ganin ba wata nasara da aka samu daga kungiyar suka ji ya zama tilas su fita daga cikinta, har dai yanda kungiyar ke musu barazana da cigaban ƙasashensu” inji shi.


Ya ƙara da cewa inshaAllah su Tinubu zasu tabbatar da ƙarin maganar da Hausawa ka cewa “Dan hakin da ka raina, shi zai tsone maka ido” inda ya kara da cewa wanga dan hakin har ƙwalƙwale idonsu maqiya zai yi.



Sai dai tun bayan hirar tasa da yayi a manyan yaruka na kasa guda uku, wato Hausa, Djerma, da kuma français, wasu ƴan ƙasa ke martani da cewa “an cema kare ana buki a gidanku, yace mu gani a kasa” ma'ana su dai ayi aiki ba surutai ba.


Allah ya taimaki Nijar 

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)