Farashin masara da dawa ya yi rugu-rugu a kasuwar hatsi ta Faskari inda kusan dubu goma ta zabge a kowane buhu a yadda ake sayar da su a baya
Farashin buhunan hatsi na yau Talata ya sakko sosai a kasuwar Faskari jihar Katsina, musamman farashin masara da na dawa
Kamar yadda Katsina Daily News ta samo farashin na yau kai tsaye daga kasuwar hatsi ta Faskarin inda ɗaya daga cikin manyan dilalan saye da sayar da hatsi na kasuwar Saifullahi Muhammad Gora ya bayyana mana kamar haka;
Buhun Masara yau an sayar da ita N47,000 a satin da ya gabata an sayar da ita N57,000 yau an sami ragin wajen dubu goma cas
Buhun Dawa, N39,000 zuwa N40,000 a wancan satin da ya gabata, an sayar da ita N48,000, an sami ragowar sama da dubu bakwai
Buhun Gero N47,000 a kasuwar baya ana sayar da shi N50,000
Buhun Dauro/Maiwa N53, 000 a kasuwar da ta wuce kuwa N55,000
Buhun Samfarerar shinkafa mafi kololuwa an sayar da ita a akan N33,000 a kasuwar baya har N40,000 ta kai
Buhun farin wake N75,000 mai kyau da ya cika sosai ya kai har N80,000 a kasuwar baya an sayar da shi har sama da N85,000
Buhun waken soya N55,500 shi ne kadai farashinsa bai sauya ba a wannan ranar
Wasu na ganin saukar farashin kayan abincin bai rasa nasaba da rashin kuɗi a hannun talakawa, yayin da kuma wasu ke ganin matakan da gwamnonin Arewa suka fara dauka ne kan yan kasuwa, na cewa ko su fito da hatsin da suka saya suka ɓoye su mai do shi kasuwa don al'umma su sami sauki, ko kuma su saka kafar wando daya da su, na daya daga cikin dalilan da ya da hatsin ya fara yo kasa a wannan satin.