🔴 INA LABARIN ZINARIYAR NIJAR DA AKA KAMA A ƘASAR ETHIOPIA ?!🇳🇪
Cikin watan da ya gabata ne, hukumomin kasar Ethiopia suka kama zinariya kimanin kilo dubu daya da ɗari hudu wato 1,400kg a filin jirgin saman ƙasar a kan hanyar wucewa da ita Dubai.
Hukumomin ƙasar ta Ethiopia sun tabbatar da zinariyar yar asalin yankin ƙasar Nijar ce, kuma zata yi kudi kimanin million dari na dalar Amurka ($100m) wato miliyar sittin na Cfa (60 milliards).
Sai dai tun bayan wannan, hukumomi a ƙasar Nijar suka dakatar da lasisin haƙar ma'adinai a kasar, wanda yayi sanadiyyar rashin aiki ga dubban matasa.
Amma cikin abin yabawa da ake ganin gwamnati tayi shi ne, dakatar da ma'aikata kusan ɗari da aka kama da hannun a cikin harƙarlar, tare da shan alwashin yin bincike akansu.
Sai dai yanzu abinda ƴan ƙasa ke tambaya kuma su ke da haƙƙin sani shi ne;
Wai ina labarin zinariyar da aka kama?
An maidota ko tana can?
Su wa ke da zinariyar?!
Muna buƙatar hukumomi su amsa ma ƴan Nijar wadannan tambayoyin!