Kasashen mulkin soji 3 na shirin kafa kungiyar haɗin gwiwa tare da samar da kuɗin bai-ɗaya
Kasar mali, Burkina Faso, da Nijar sun gabatar da tattauna a babban birnin Burkinabe don samar da matsayi na haɗin gwiwa tsakanin kasashe masu mulki soja, taron ya gudana ne a ranar Alhamis.
Sunyiwa kungiyar laƙabi da Alliance of Sahel States (AES), a kwanakin baya ne dai kasashen uku su cimma matsaya na ficewa daga kungiyar ECOWAS.
sai dai wasu na ganin babban barazana ce ga Najeriya ta fuskan tsaro rashin samun kyakyawar alaƙa da kasar ta Nijar a wasu jihohi da suyi iyaka da kasar. Haka zalika kasashen sun bayyana cewa, zasu samar da kuɗin bai ɗaya na ƙasashen uku hakan shine zai kara tabbatarwa duniya cewa, sun fita daga ƙangin bauta.
Menene mafita ?