Me mu ke tsoron ya bayyana ga sojojin da su ka yi juyin mulki a Nijer 🇳🇪 nan gaba?
Na karanci rahoton BBC Hausa duka na yadda tsohon Jakadan Faransa Nijer ya yi zargin cewa; akwai sa hannun Tsohon shugaban ƙasa Isoufou Mahamadu wajan tumbuke abokinsa a mulki Mohamed Bazoum. Na yi mamakin yadda Mahamadu Isoufou yake ɗanawa da Faransa a lokacin mulkinsa amma su ka fito ƙarara su ka yi masa wannan zargin kai tsaye, wanda ƴan Nijer da dama tuni sun jima suna masa wannan zargin. Duk da shi jakadan zai iya faɗar komi tunda an amsa korar kare.
Ba shakka tun bayan hawan bazoum PNDS tarraya ta samu babbar ɓaraka a tsakaninsu. Musamman da Bazoum ya zo da wani salo mai kyau, na kusantar talaka da hana ɓaɓakere da dukiyar ƙasa da kuma hana ƴan jam'iya yin duk abinda su ka ga dama, irin farko. Da naɗa waɗanda ba su cancanta ba a muƙamai. Tun daga nan ya fara samun marsaloli da wasu ƴaƴan jam'iyarsa, saboda ya toshe wasu hanyoyi na bushasha da dukiya. Daga nan aka hana shi sukuni a jam'iya, ƙarshe kusantar talakawan ya rage, (Ba wanke bazoum nake daga laifi ba, amma duk in da gaskiya ta zo a faɗe ta) duk wata hujja da za a baka ƙwaƙƙara ta dalilin yin wannan juyin mulki, to sai ka ji hujjar yin hakan shi ne matsala ce, da Rikici da ya samo asali daga jam'iya ko kuma wajan rabon muƙamai da kuma abin Duniya.
To tsoron da mu ke waɗannan sojojin a wayi gari a ce; wannan juyin mulki ba don ƙasa aka yi ba, an yine don biyan wasu buƙatun ƴan siyasa ba an yine don a fidda ƙasar daga dabaibayin da ya dabaibaye taba. In an yi hakan tabbas (An ci amanar Bazoum) to amma fa a tafiyar har yanzu bamu gano hakan ba, abinda mu ka gano da Abinda ya bayyana mana a yanzu, akwai alamun an yi don ƙasa ne, da samun cikakken inci, to amma ba mu san nan gaba mi zai bayyana ba. Allah ya tabbatar mana da alheri.
Allah ya sa mu dace.