No title

Mr blogger
0

  NIJ


AR BA TA JANYE DUKA SOJOJINTA BA DAGA DAKARUN HAƊIN GWUIWA NA ECOMOG ~ INJI CHRISTOPER MUSA


Shugaban dakarun sojan Nijeriya, liteunant general Christopher musa ya sanarwa Aljazeera cewa duk da rashin fahimtar dake tsakanin Ecowas da sojojin mulki na Nijar bai sakasu janye dukan sojojin su dake cikin dakarun haɗin gwiwa, “saboda sun san da cewa ƙasa daya ba zata iya fuskantar matsalar tsaron wannan yankin ba” inji shi.



Ya ƙara da cewa “Sojojin Nijar ɗin dai suna cigaba da rike gefen da aka wakkala musu a yankin tafkin Chad wato lake Chad, tare da sauran takwarorinsu na Nijeriya, kameru, da Chad.


Ya kuma bayyana fatarsa akan duba zancen sake komawa kungiyar Ecowas daga wadannan kasashen uku na AES, inda yace “Tabbas Ecowas za ta yi zama da duka ƙasashenta, kuma za ta nunawa wadannan kasashen na Nijar, Burkina da Mali muhimmanci zamansu a Ecowas domin cigaba da ƙarfafa tsaron yanki”.


Me k


uke fatan ku ga an cimma a Babban taron na Ecowas da ake sa ran yi a nan gaba kaɗan?

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)