Yadda 'yan Kannywood suka shiryawa Ali Nuhu liyafar Taya shi Murnar zama Shugaban Masana'antar fina-finai ta kasa Baki Daya .
Daga:
Tajuddeen Shuaibu koki.
A jiya ne masana'antar kannywood da kanta ta gudanar da biki na musamman domin taya Shugabansu kuma jagoransu Ali nuhu murna bisa mukamin daya samu na shugaban film Na Nigeria Baki Daya Kannywood and Nollywood e t.c.
Wannan biki ne na musamman wadda ba'a taba irinsa a Masana'antar kannywood ba, domin kusan duk 'Yan wasan hausa kwansu da kwarkwatansu,da manyan mawakan nigeria baki daya.,duk sun hadu a wannan wajen Taron.
Ali Nuhu ya kasance Uba, Da ,Yaya ,Kani ga kusan dukkan Abokan sana'ar sa .ya samu shedar iya muamila da kuma kyautatawa na kasa da shi ,sannan dayawan Matasan Kannywood Maza da Mata Ali Nuhu ne ya Raine su ,kuma dayawan su suna masa sheda da cewa Mutum ne me kamun Kai da tsawatarwa idan yaga zaayi abinda be dace ba .