EFCC ta Kwato 32 Biliyan da $445,000, Daga Hannu Betta Edu, Sadiya Umar Farouq, da Halima Shehu

Mr blogger
0

 EFCC ta Kwato 32 Biliyan da $445,000, Daga Hannu Betta Edu, Sadiya Umar Farouq, da Halima Shehu



Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) tana binciken ministar jin kai Betta Edu, da tsohuwar ministar jin kai, Sadiya Umar-Farouq, da ko’odineta na Hukumar inshorar jama’a, Halima Shehu. Ya Zuwa yanzu an kwato jimillar Naira biliyan 32.7 da dala 445,000 Daga hannun su.



Hukumar ta bayyana hakan ne a yau Lahadi ta hannun jami’anta dangane da yadda ake ta yada jita-jita game da ci gaban binciken da ta ke yi kan almubazzaranci da kuɗaɗe a ma’aikatar kula da jin kai, da magance bala’o’i da ci gaban al’umma.


“A farkon binciken hukumar ta gayyaci jami’an ma’aikatar jin kai da aka dakatar dasu daga baya da kuma wadanda aka dakatar, Binciken da aka yi a kan badakalar da aka samu an kwato naira biliyan 32.7 da dala 445,000 zuwa yanzu.



“Bincike na Gaskiya da EFCC ta Gudanar ya gano ƙarin wasu makudan kudade da suka hada da kuɗaɗen Covid-19, lamunin Bankin Duniya da sauransu.


“Bugu da kari, EFCC ba ta wanke duk wani da ake zargin yana da hannu a badakalar ana ci gaba da Gudanar da bincike kan lamarin.



Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)