Hukumar EFCC Tana zargin ma’aikatan banki a Najeriya Da haɗa baki da jami’an Gwamnati wajen sake wawure kudaden da aka Karbo Daga Hannun Marigayi Janar Sani Abacha.

Mr blogger
0

 Hukumar EFCC Tana zargin ma’aikatan banki a Najeriya Da haɗa baki da jami’an Gwamnati wajen sake wawure kudaden da aka Karbo Daga Hannun Marigayi Janar Sani Abacha.



A watan Disambar 2017, Gwamnatin Tarayya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da ƙasar Switzerland dangane da mayarwa da kuma lura da dala miliyan 322 na dukiyar Abacha. Waɗannan kuɗaɗe an Samar su ne don Transfer Cash Conditional Cash a ƙarƙashin shirin Social Investment wanda aka fara a watan Disamba 2016 lokacin Gwamnatin Tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.



Kuɗaɗen da aka wawashe an ware su ne domin samar da alawus-alawus na Naira 5,000 duk wata ga ‘yan Najeriya masu rauni. Sai dai mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar A Yau Lahadi cewa hukumar ta fara gudanar da bincike kan wasu almundahanar kudi da ake zargin ma’aikatar. Wadannan sun hada da yin amfani da kuɗaɗen COVID-19 da kuma karkatar da rancen da Bankin Duniya ke bayarwa wanda ma'aikatar jin kai ta hada kai don taimakon talakawan Najeriya.



Hukumar ta EFCC ta jaddada cewa binciken da ta ke yi Ta gano wani tsari na yaudara. Ta bayyana cewa ana gudanar da bincike a kan bankunan dake da hannu a zamba, kuma manajan daraktocin waɗannan bankunan sun bayar da bayanai masu amfani. Wadanda aka samu da laifi za su fuskanci hukunci A Cewar EFCC.



Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)