Kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta yi nadamar zaben shugaban kasa Bola Tinubu a 2023. Daga cikin manyan ‘yan takarar shugaban kasa uku a zaben 2023, Tinubu, wanda ya tsaya takara a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya samu mafi yawan kuri’u daga arewacin Najeriya

Mr blogger
0

 Kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta yi nadamar zaben shugaban kasa Bola Tinubu a 2023. Daga cikin manyan ‘yan takarar shugaban kasa uku a zaben 2023, Tinubu, wanda ya tsaya takara a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya samu mafi yawan kuri’u daga arewacin Najeriya



 A wata hira da jaridar Guardian A Yau Talata, Abdul-Azeez Suleiman, mai magana da yawun kungiyar, ya bayyana cewa "Arewa ta yi kuskure wajen zaben Bola Tinubu a zaben Shugaban ƙasa a 2023, kuma da wuya su sake maimaita kuskuren nan gaba." Ya kuma jaddada cewa Arewa ta koyi darasi daga wannan kuskuren da aka yi a baya, kuma za ta kara taka tsantsan wajen zabo dan takarar da zai hada kan kasar nan tare da gudanar da mulki domin maslahar ‘yan Nijeriya baki daya.


Dangane da sukar da ake yiwa gwamnatin Tinubu kan manufofinta na kin jinin talakawa, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, babban mai kalubalantar Tinubu a zaben da ya gabata, ya yi tsokaci a farkon makon cewa manufofin shugaban kasa ba su da fuskar dan Adam, musamman a kan batun kudin wutar lantarki. Duk da haka, Tinubu ya sha ba wa ‘yan Najeriya tabbacin cewa gwamnatinsa ce ke da iko kan lamarin kuma kwanaki masu kyau na gaba.


Bayan rattaba hannu kan kudirin lamunin dalibai, Tinubu ya bayyana fatansa game da makomar yaran Najeriya, inda ya jaddada muhimmancin ilimi wajen yaki da talauci. Ya kuma yi tsokaci kan matsalolin tattalin arziki, inda ya bayyana cewa, ana daukar matakan shawo kan hauhawar farashin kayayyaki da kuma inganta fannin hada-hadar kudi, da nufin dawo da martabar Najeriya a duniya.



Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)